EFCC ta gurfanar da Alex Badeh a Kotu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Air Marshal Alex Badeh mai ritaya, ya gurfana a babban kotu a Abuja.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta gurfanar da tsohon Babban hafsan sojin Najeriya, Air Marshal Alex Badeh, mai ritaya a babbar kotun Abuja.

Hukumar ta zargi Mista Badeh da laifin satar kudi mallakin Rundunar sojin sama ta Najeriyar kimanin dala miliyan 14, a lokacin da yake babban hafsan sojin kasar, domin sayen filaye.

Rahotanni sun ce Mista Badeh ya gina katafaren gida na kasaita har ma da rukunin shaguna.

Mista Badeh dai ya musanta wannan zargi.

Air Marshal Badeh mai ritaya shi ne tsohon babban hafsan sojin Najeriya karkashin mulkin shugaba Goodluck Jonathan.

Yana daga cikin wasu manyan jiga-jigan tsoffin sojojin kasar da EFCC ke gudanar da bincike a kansu, bisa zarginsu da almundahana.