Shugabannin EU na taro kan 'yan gudun hijira

Image caption 'Yan gudun hijira na fuskantar matsaloli da dama

Shugabannin Tarayyar Turai da na Turkiyya suna gudanar da wani taron koli a Brussels, domin shawo kan matsalar 'yan gudun hijira mafi girma da aka taba fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu.

An samu sabani tsakanin shugabannin Tarayyar Turan gabanin fara taron, inda a yayin da Tarayyar Turan ta shirya sanar da rufe babbar hanyar kwararar 'yan gudun hijira ta kudancin yankin Balkan, shugabar gwamnatin Jamus kuwa, Angela Merkel, nisanta kanta ta yi daga matakin.

Firayi ministan Turkiyya Ahmet Davutoglu, ya ce dukkan bangarorin biyu dai, suna da muhimmanci ga ci gaban juna, kuma makomar nahiyar tasu, ta dogara ne a kan kyautatawa.

Shi ma shugaban majalisar dokokin Tarayyar Turan, Martin Schulz, ya ce manufar taron ba za ta zama ta rufe kofa ga 'yan gudun hijira na gaskiya ba.

Karin bayani