Nigeria ta gana da Afrika ta Kudu kan tsaro

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Mansur Dan-Ali, Ministan harkokin tsaro na Nigeria

Ministocin tsaro na kasashen Najeriya da Afrika ta kudu sun yi wata ganawa a yau a Abuja babban birnin Najeriya.

Mansur Muhammad Dan'ali da Nobise Mapisa Nqakula sun tattauna kan fannonin hadin kai ta fuskar tsaro tsakanin kasashen biyu wadanda ke daga cikin kasashen da suka fi karfin soji a nahiyar Afrika.

Ganawar ta zo ne mako daya bayan wata ziyarar aiki ta farko da Dan-Ali ya kai Afrika ta Kudun , inda ya tattauna a kan yiwuwar hadin gwiwar kasashen biyu a kan harkar tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar ta Afrika baki daya.

Kasar ta Najeriya ta shafe shekaru tana fuskantar matsalar Boko Haram, ko da yake sojojin kasar na cewa sun ci galabar matsalar.