Nigeria za ta shiga kawancen yaki da ta'addanci

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kasar za ta shiga wata rundunar hadaka da Saudiyya ke jagoranta da nufin yaki da kungiyar IS.

Shugaba Buharin ya ce, shiga wannan hadaka za ta taimaka wa yakin da Najeriya ke yi da kungiyar Boko-Haram wadda take ikirarin alaka da kungiyar IS din.

Sai dai kuma wasu masu sharhi na ganin shiga wannan hadaka na iya jefa Najeriya cikin rikicin da ke tsakanin manyan kasashen duniya.

Gwamnatin Najeriya da dakarun sojin kasar sun zage dantse a yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram da ta addabi arewa maso gabashin kasar, da kasashen makofta irin su Nijar, da Kamaru da kuma Chadi.