Wani ya yi kisa a kan Messi da Ronaldo

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

An kama wani dan Nigeria da laifin kisan wani abokin shi bayan sun yi musu a kan 'yan wasan kwallo, in ji 'yan sanda a India.

Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ce lamarin ya faru ne bayan abokan sun yi musu a kan ko wanene ya fi iya kwallo a duniya tsakanin Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo.

A ranar Lahadin da ta wuce ne dai Michael Chukwuma mai shekara 21 ya soki Obina Durumchukwu mai shekara 34, a garin Nallasopara da ke wajen birnin Mumbai da ke arewacin indiya.

Abokan biyu sun hadu a daren ranar Asabar domin bikin murnar zagoyowar ranar haihuwar mista Durumchukwu', amma a safiyar ranar Lahadi sai su ka yi musun da ya jawo ajalin Obinan.

Daya daga cikin abokan yana goyon bayan, Messi, dan wasan kungiyar Barcelona dayan kuma na goyon bayan Ronaldo, dan wasan kungiyar Real Madrid.

Marigayi Obina ne ya jefi mista Chukwuma da kwalaba a fuskarsa kuma ta fashe ta ji masa rauni, yayin da shi kuma Chukuma ya caka wa Obina kwalbar, abin da ya yi ajalinsa.