Farashin mai ya dan tashi a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Farashin mai ya yi ta faduwa a watannin baya

Farashin danyen man fetur samfurin Brent Crude ya tashi a kasuwannin duniya, inda ya kai dala 40 kowacce ganga daya.

Farashin ya karu da kashi 40 cikin 100 karo na farko tun bayan da ya fara faduwa a watan Janairu.

Ana ganin tattaunawar da ake yi tsakanin manyan kasashe masu samar da man ne ya yi sanadin tashin farashin.

Har yanzu dai ba a cimma wata tsayayyiyar yarjejeniya ba, amma manyan kasashe masu samar da man za su gana a Moscow cikin wannan wata na Maris.

Karin bayani