Sojin Tunusia sun kashe masu ta da kayar baya

Image caption Tunusia tona katon rami a kan iyakarta da Libya don hana 'yan ta'adda shiga

Dakarun tsaro na Tunisia sun hallaka masu tayar da kayar baya 21 bayan da suka kaddamar da wani hari a tsakanin kan iyakar kasar da ta Libya.

Fadan ya biyo bayan wani hari ne da aka kai sansani soji da kuma ofishin 'yan sanda a garin Ben Guerdane, da ke gabashin kasar.

Ministan harkokin cikin gida na kasar ya kuma ce an kashe fararen hula hudu a fafatawar.

Tunusiya na fuskantar barazanar tsaro daga masu tayar da kayar baya da ke da sansani a Libya.

Firai Ministan Tunusiya Habib Essid, ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, a makon da ya gabata ma dakarun kasar sun kashe masu tayar da kayar baya biyar a kan iyakar kasar da Libya bayan da suka shiga kasar da niyyar kai hare-hare.

Karin bayani