Sojin Amurka sun kashe 'yan Al-shabab

Mayakan Al-shabab Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar Al-shabab ta dade ta na kai hare-hare a kasar Somalia da kassahe makofta.

Rundunar Sojin Amurka ta yi cikakken bayani a kan wani mummunan harin da ta ce ta kai kan kungiyar Al shabab a kasar Somalia ta sama.

Rundunar ta ce ta yi nasarar halaka 'yan kungiyar Al shabab din sama da 150, a wani sansanin horar da 'yan kungiyar a ranar Asabar din da ta gabata.

Rundunar Sojin Amurkan ta ce ta ce dakarunta sun yi amfani da jiragen yaki masu matuka da kuma marasa matuka wajen kai harin a kan sansanin da ke da tazarar kusan kilomita 200 daga Mogadishu, babban birnin kasar, a daidai lokacin da mayakan Al shaban din ke shirin kai hari.

Kakakin fadar White House Josh Earnest ya ce mayakan na shirin fita daga sansanin ne don kai hari, kuma suna barazana ga dakarun Amurka da na tarayyar Afurka.

Babu dai wani martani daga kungiyar Al shabab.