Shugaba Zuma ya iso Nigeria

A yau ne Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu zai fara ziyarar aiki a Najeriya.

Makasudin ziyarar shi ne dan karfafa alaka tsakanin kasashen biyu, ta fuskar ayyukan noma, da hako ma'adinai da sauran su.

Yayin ziyarar kuma ana sa ran shugaban biyu za su tattauna akan dangantakar kasashen, wadda ta dan yi tsami a baya-bayan nan.

Harwayau, za su tattauna akan yadda za a budewa 'yan Najeriya kofar da za su kafa kamfanoni da masaba'antu a kasar Afurka ta Kudu kamar yadda suka samu dama a Najeriya.

Sai batun karfafa tsaro, ganin yadda Afurka ta Kudu ta kware wajen kera makamai da saida su.

Malam Garba Shehu, Mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari ne a kan al'amuran yada labarai, ya yi bayani a kan ziyarar ta Mista Zuma, inda shima Malam Bala Muhammad mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Najeriyar, kuma ya hira da abokkin aikinmu Muhammad Kabir Muhammad a kan ziyarar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti