Benin: Zinsou zai fafata da Talon

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Boni Yayi ya kusa sauka daga shugabancin kasar Benin

Firai ministan kasar Benin, Lionel Zinsou, zai fuskanci abokin hamayyarsa dan kasuwa, Patrice Talon, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, kamar yadda sakamakon wucin gadi ya nuna.

Tilas ne kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da sakamakon tukunna.

Ana ganin kuma za a samu wani babban kalubale, musamman yayin da wani dan kasuwar, Sebastien Ajavon, ya samu kasa da kashi biyu cikin 100 a bayan Mista Talon.

Ya zama tilas ne a je zagaye na biyu na zaben saboda kuri'un sun kasu tsakanin 'yan takara 33 wadanda ke fatan gadar Thomas Boni Yayi, wanda zai sauka bayan wa'adin mulki biyu.