Abubuwa biyar da ya kamata ka sani a kan Sharapova

Tsohuwar 'yar wasan Tennis ta daya a duniya, Maria Sharapova ta bayyana cewa wani gwaji da aka yi mata a lokacin gasar Australia Open ya gano cewa tana ta'ammali da kwayoyi masu sa kuzari.

Tana shekara 14 ta zama kwararriya
Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Maria Sharapova: 'Yar wasan Tenni

Sharapova ta fara wasan Tennis ne tun tana yarinya, kuma a lokacin da kai shekara takwas tana daga cikin 'yan wasan Tennis da suka halarci bikin nuna 'yan wasan da aka yi a birnin, Moscow inda aka nuna gwarzuwar 'yar wasan Tennis, Martina Navratilova.

Tana da shekara tara ne kuma ta fara zuwa makarantar koyon wasan Tennis ta Nick Bollettieri's da ke Florida tare da babbanta Yuri.

Mahaifiyarta Yelena, ta kasance a Siberia na tsawon shekaru biyu ba tare da Sharapova da mahaifinta ba, saboda takunkumin hana biza.

Ba a wani dade ba mista Bollettieri ya gano kwazon matashiyar, kuma tana da shekara 14, ta zama kwararriya.

A shekarar 2015 kadai ta samu kusan $29.5 miliyan

'Yar wasan tennis din, mai shekara 28, ita ce mace 'yar wasan motsa jikin da ta fi kowa daukar albashi mai tsoka a duniya a shekaru 11, in ji mujallar Forbes.

Kudadden da ta samu a wasan Tennis kadai sun kusa $29.5 miliyan, kuma tana da kwantiragi da kamfanin ruwa na Evian da kamfanin Agoguna na Tag Heuer da kamfanin mota na Porsche da kamfanin kayan kwalliya na mata na Avon da kuma kamfanin kayan sakawa da takalmin 'yan wasa na Nike.

Duk da cewar bayan ta amsa cewar ta yi amfani da kwayoyin kara kuzari, kamafinin Nike ya soke kwantiragin da ya bata a alakar da suka kulla tun tana da shekara 11.

Kamfanin agoguna na kasar Swistzerland na Tag Heuer, shi ma ya ce zai yanke hulda da gwarzuwar 'yar wasan Tennis din.

Ta ci manyan kyaututtuka na yabo guda biyar
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Maria Sharapova: 'Yar wasan Tennis

'Yar wasan Tennis din ta zama mace ta uku mai karancin shekaru da ta ci kofin gasar Tennis na Wimbledon a lokacin tana da shekara 17 a shekarar 2004, kuma a shekarar da ta biyo baya ne ta zamo 'yar wasan tennis ta farko a duniya.

A shekarar 2006, ta ci gasar Tennis na Amurka kuma ciwon da ta ji a kafada bai hana ta samun matsayi na uku a gasar Melbourne a shekarar 2008 ba.

Sai dai, rashin lafiyarta ta jawo mata komabaya a wasan, domin a karshen 2010 ne kuma ta koma ta 18 a duniya.

A shekarar 2012, sai ta farfado ta koma sama bayan ta doke Sara Errani, inda ta ci gasar Tennis na Faransa a birnin Paris.

Sun zaune a kusa da Chernobyl
Hakkin mallakar hoto epa

Mutanen gidansu sun zauna a wani wurin da ke da nisan kilomita 130 daga tashar wutar lantarki ta Chernobyl, a lokacin da daya daga cikin na'urar tashar ta fashe a shekarar 1986. Iyayensu sun tsere daga nan a lokacin mahaifiyarta na dauke da cikinta.

Sannan suka tare a wani karamin gari Nyagan da ke Siberia, inda aka haifi Sharapova kuma ta taso.

Ta bayar da taimakon kudi a yankin Gomel na birnin Belarus wanda fashewar na'urar tashar Chernobyl ta shafa.

An samu kwayar meldonium a gwajin da aka yi mata
Hakkin mallakar hoto epa

A ranar bakwai ga watan Maris ne gwarzuwar 'yar wasan Tennis din ta sanar da cewa an samu kwayar meldonium a gwajin da aka yi mata, maganin da ake amfani da shi ga masu fama da cutar angina, wanda ke takaita jinin da ke shiga jikin mutum.

Sharapova ta ce "Gwajin da aka yi mini an gano maganin kara kuzari, kuma na dauki dukkan alhakin sakamakon gwajin."

Ta ce "Na shafe tsawon shekara 10 ina shan kwayar meldonium, bayan likitan iyali da ke duba mutanen gidanmu ya bani, saboda matsalolin lafiya, amma na san maganin a matsayin mildronate ne.

Ta kara da cewar a baya-bayan nan ne ta gano cewar kwayar tana da wani suna na daban wato meldonium, kuma a kwanan nan ne aka saka shi a jerin sunayen da hukumar da ke hana 'yan wasa ta'ammalin da kwayoyin kara kuzari na duniya ta hana amfani da su.

Kungiyar wasan Tennis na duniya ta ce za a dakatar da 'yar wasar Tennis din daga 12 ga watan Maris.

Ta ce "Na yi babban kuskure tare da watsa wa magoya baya na da ma wasan Tennis din kasa a ido, tun ina da shekara hudu nake wasan Tennis da nake matukar kauna."

"Na san wannan zai zo min da wasu sakamakon kuma bana so na kawo karshen aiki na ta haka. Ina matukar fatan zan samu wata damar domin buga wannan wasa."