India: An yi wa yarinya fyade an konata

Image caption Matan Indiya na yawan fuskantar matsalar fyade

Kashi 80 cikin 100 na wata yarinya 'yar shekara 15 a Indiya ya kone bayan da aka yi mata fyade aka kuma cinna mata wuta kusa da Delhi babban birnin kasar.

'Yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi, wanda suka ce yarinyar ta san shi.

Sun shigar da tuhumar fyade da kisan kai da suke masa.

A na ci gaba da fafata muhawara a kasar kan fyade tun bayan da wani gungun mutane suka yi wa wata daliba fyade a cikin motar bas shekaru uku da suka gabata, wanda ya jawo matukar fushin 'yan kasar.

Karin bayani