Ese: Lauyoyi za su kare Yunusa Yellow

Gwamnan Dickson na Bayelsa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Batun na Ese da Yususa dai ya janyo zazzafar muhawara a a shafukan sada zumunta da muhawara a Najeriya.

Yayin da aka gurfanar da matashin nan da ake zargi da tafiya da wata yarinya daga jihar Bayelsa zuwa Kano wato Yunusa Dahiru wanda aka fi sani da Yunusa Yellow, wasu lauyoyi sun ce za su tsaya masa a shariar da aka fara yi masa a wata kotun gwamnatin tarayya da ke birnin Yanagoa na jihar Bayelsa.

Ana dai tuhumar matashin ne da sace Ese da tilasta mata shiga musulunci, amma ya musanta.

Su dai lauyoyin sun ce za su tsayawa matashin ne dan tabbatar da cewa ya samu adalci a shari'ar da aka fara yi masa.

Bulama Bukarti na daga cikin lauyoyin da za su tsayawa Yellow, ya ce abinda ya ja hankalin su da har za su kare matashin, shi ne an nuna tamkar Yunusa ba shi da gata saboda kusan jama'a sun karkata ne a bangaren Ese.

Alhalin tun da fari ita da kanta ta ce ba sace ta Yunusa ya yi ba, haka kuma ba bakon fuska ba ne ga iyalan Ese.