'Yan BH sun kai wa sojin Nigeria hari a Gwoza

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Sojojin Nigeria sun fatattaki 'yan Boko Haram daga wuraren da suka mamaye a baya da yawa

Rahotanni a Najeriya na cewa wasu da ake tsammanin 'yan Boko Haram ne sun kai wa sojojin kasar da ke garin Pulka, na karamar hukumar Gwoza hari a daren Litinin.

Ko da yake rahotannin wasu jaridu sun bayyana cewar fadan ya faru ne a garin Bita, inda suka fuskanci tirjiya daga sojin na Najeriya.

Hakan a cewar rahotannin ya sa hukumar soji ta tura da jiragen yaki don kai wa sojojin dauki.

Malam Mohammed Gwoza, wani dan asalin yankin ne da ke bin diddigin abun da ke faruwa, ya kuma yi wa Aminu Abdulkadir karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai harin, inda ta ce mayakan Boko Haram masu tserewa daga Dajin Sambisa ne suka kai wa sojojin hari daga bangarori uku na Damboa da Tokumbere da Pulka.

Sai dai sanarwar ta ce sojojin sun dakile hare-haren, har ma biyu daga cikin mayakan Boko Haram din sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harbinsu da aka yi.