Korea ta Arewa ta kera sabbin makaman roka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Kim Jong-un

Shugaban kasar Korea ta Arewa, Kim Jong-un ya yi ikirarin cewa masana kimiyyar kasar sun yi nasarar kera wasu kananan makaman nukiliya, wadanda za a iya goya su jikin roka.

Kamfanin dillancin labaran kasar ne ya wallafa wannan labari tare da wasu hotunan da ke nuna shugaban kasar yana tsaye kusa da wani mulmulallen karfe.

Wakilin BBC ya ce da wuya a tabbatar da gaskiyar wannan ikirarin, amma ya bayyana cewa Koriya ta arewar ta shammaci duniya a baya, lokacin da ta baje-kolin wasu na'urorin fasaha, wadanda ba wanda ya zata masana kimiyyar kasar sun iya kera su.

Koriya ta arewar dai na da makami mai linzami, ko rokokin da za su iya cim ma Koriya ta kudu da Japan da kuma wasu sansanonin Amurka da ke yankin Pasific