Amurka ta daukaka karar Apple

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Apple na fuskantar shara`a

Kamfanin Apple na fuskantar shara'a da gwamnatin Amurka don tilasta masa bude makullin sirrin waya

Mahukunta a Amurka sun daukaka kara dangane da hukuncin da wani Alkali ya yanke cewa ba za a tilasta wa kamfanin Apple ya bude sirrin wayar iPhone ta wani da aka masa shara'ar da ta shafi miyagun kwayoyi ba.

Ma'aikatar shara'ar Amurkar da ta dogara ne da dokar da ta ki ba da damar bude wayar dan bindigar nan da ya kai harin San Bernardino.

Yanzu dai Amurkar ta daukaka kara zuwa wata babbar kotu, bayan hukuncin da Alkalin kotun farko ya yanke cewa ba shi da ikon ba da umurni ga kamfanin Apple domin ya bude sirrin waya.

Kamfanin Apple dai ya yi kukan cewa bude sirrin wayar zai zama babbar barazana ga al'amuran da suka shafi kariya da kuma sirrin jama'a, kuma yin hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Amurka.

A karar da ta shigar tun da farko, Amurka tana so ne a bude wayar iPhone din Jun Feng ne, wanda ya amince da aikata laifin safarar methamphetamine domin a bankado abokan huldarsa da sauran mutanen da suka aikata miyagun laifukan tare.