Ana daukar cutar Zika ta Jima'i

Uwa da Jaririn ta da ke dauke da cutar Zika Hakkin mallakar hoto Flavior Former
Image caption Cutar Zika na janyo tawaya a kwakwalwar Jarirai.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta gargadi mata masu juna biyu da su kaucewa zuwa yankin Latin Amurka da cutar Zika ta barke a wurin, saboda ana samun karuwar bayanai da ke kara alakanta cutar da samun tawaya wajen haihuwa.

WHO ta kara da cewa, rahotannin da suke fitowa daga sauran kassahen da cutar ta bulla, na nuna ana daukar cutar a lokacin Jima'i ba kamar yadda aka yi zato a baya ba na cewa ba a iya daukarta ta wannan hanya.

Hukumar ta kara da cewa, mata masu juna biyu da ya zama dole su yi balaguro, su tabbatar sun yi binciken wuraren da za su je dan daukar matakan kare kai.

A watannin da suka gabata ne kwayar cutar Zika da wani nau'in sauro ke yadata, ta watsu a wasu sassan Latin Amurka.

Haka kuma bincike ya nuna, daya daga cikin matsalolin da cutar ke haifar wa shi ne ta na janyo tawaya a kwakwalwar jarirai.