Zimbabbwe: Gwamnati za ta biya manoma diyya

Shugaba Mugabe
Image caption Shekaru 16 da suka wuce ne gwamnati ta kwace gonakin.

Rahotanni daga Zimbabwe na cewa gwamnatin kasar na shirin biyan diyya ga manoma farar-fata da aka kwace musu gonakai a wata mamayar da gwamnati ta yi shekaru 16 da suka wuce.

Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya ruwaito cewa Ma'aikatar kudin kasar ta fitar da wata sanarwar da ke cewa za a biya Manoman wasu kudade da suka shafi gonaki da kuma na'urorin da suka yi asararsu.

Idan wannan yunkuri ya tabbata, to shugaba Mugabe zai lashe amansa kenan, kasancewar a baya ya ce ba gwamnatin kasar ba ce za ta biya diyyar gona ko filaye ba.

Kasar Zimbabwe dai na duba hanyoyin kyautata dangantaka ne da Hukumar ba da lamuni ta duniya da sauran cibiyoyin da ke hada-hadar kudi.