Sarauniya ta kai karar jaridar The Sun

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sarauniya ta ce al'ummar Biritaniya ne za su yanke shawara da kansu

Fadar Buckingham ta Ingila ta kai kara wajen hukumar da ke sa'ido a kan kafafen yada labarai, bisa wani labari da aka wallafa a jarida a kan cewa Sarauniya Elizabeth na goyon bayan Biritaniya ta fice daga kungiyar tarayyar Turai watau EU.

A shafinta na farko, jaridar The Sun ta rubuta cewa Sarauniya ta bayyana matsayinta ne a lokacin wata mahawara tsakaninta da tsohon mataimakin Firai minista Nick Clegg, a shekara ta 2011.

A cikin watan Yuni ne za a yi kuri'ar raba gaddama a Biritaniya kan batun ci gaba da kasancewa a kungiyar ta EU.

Fadar Buckingham ta ce Sarauniya ba ta goyon bayan kowanne bangare a kan batun kuri'ar raba gaddamar da ke tafe.

Shi ma Mista Clegg ya ce ba zai iya tunawa ba ko sun yi wannan maganar da Sarauniya.