Cameron: Ana bukatar dokar gina dalbaton waya

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Firayim Ministan Birtaniya

Firayim Ministan Birtaniya ya ce akwai bukatar sauya doka domin a gina dalbatoci ta yanda za a samu signar intanet mai karfi a yankunan karkara.

Da yake tattaunawa da 'yan jarida a wani shirinsa mai suna "Prime Minister's Questions" Mr Cameron ya ce "dukanmu masu laifi ne saboda mun yi sukar yin haka a baya."

Sai dai ya jaddada cewa yayin cimma wannan burin, kamata ya yi a maida hankali wajen ganin cewa an hada kowa da intanet.

Dan majalisar dokoki Andrew Murrison ne ya fara dago wannan batu, yana cewa siginar intanet na da rauni a Birtaniya, kuma lamarin na haddasa asara ga 'yan kasuwa a yankunan karkara.

Gwamnatin Birtaniyar dai ta ce ta kama hanyar cimma burinta na samar da intanet ga kashi 95 bisa 100 na al'umar Birtaniya nan da karshen shekara ta 2017.