Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

''Tsaurin ra'ayin addini na da illa''- Izala

A Najeriya a yayin da dakarun kasar ke ci gaba da fafatawa da yan kungiyar Boko Haram, kungiyar Izala ta kasar ta ce za ta dukufa wajen kokarin wayar da kan jama'a a kan tsaurin ra'ayi ta fuskar addini.

Kungiyar dai ta ce za ta yi hakan ne ta hanyar shirya tarurruka , don wayar da kan jama'a, musamman matasa.

Ga abinda shugaban majalisar malamai ta kungiyar Izalatul bidi'a wa ikamatus sunna Sheikh Bala Lau ya shaidawa BBC;