Ginin da ya rufta a Lagos ya halaka mutane 30

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wani bene da ya rufta a Lagos a shekarun baya

Ma'aikatan agaji a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane a kalla 30, sakamakon ruftawar wani bene mai hawa biyar wanda ya ruguje a Lagos.

Benen wanda ba a kammala gininshi ba a yankin Lekki na masu arziki, ya rufta ne sakamakon ruwan sama mai karfi da aka sharara a ranar Talata.

Kawo yanzu an ceto mutane 13 daga cikin baraguzan ginin, sannan ana tunanin akwai wasu mutanen da suka makale.

Sanarwa daga gwamnatin jihar Lagos ta ce masu ginin sun yi ginin ne ba tare da izinin hukumomi ba, kuma tuni aka killace wurin.

A yanzu haka gwamnati ta bukaci masu ginin su mika kansu wajen 'yan sanda domin su fuskanci hukunci.