Fyade: Mata sun yi zanga-zanga a Kano

Image caption Mata na zanga_zangar adawa da fyade a Kano.

Daruruwan mata na wani tattaki na zanga-zangar lumana a Kano, domin nuna fushinsu kan ayyukan fyade da suke karuwa a jihar.

Image caption Yarinya 'yar shekaru goma na cikin wadanda ke tattakin zanga-zanga a kan fyade.

Wata yarinya 'yar shekaru goma da aka yi wa fyade na daga cikin dandazon masu tattakin.

Mahaifiyar yarinyar ta ce har yanzu 'yar tana cikin halin kunci da tsangwama da kuma firgita, sakamakon fyaden da wani mutum dan shekara 35 ya yi mata a tsakiyar watan Janairun 2016.

Mahaifiyar ta nuna matukar damuwarta, inda ta ce "Har yanzu ana gudanar da bincike a asibiti a kan 'yata, saboda ciwon da mutumin ya ji mata a hannu da baki, a yayin da ya ke mata fyaden."

Matar dai ta yi korafin cewa, 'yan sanda basu kula ta ba a lokacin da ta shigar da kara.

Kazalika kuma wasu sakamakon gwaje-gwajen asibiti da ke hannun 'yan sandan sun bata, amma tana fatan kwamishinan 'yan sandan yanzu zai kwato masu hakkinsu.

Shugabar kungiyar mata Lauyoyi ta Kano, Husaina Ibrahim, ita ce jagorar wannan zanga-zanga, kuma ta ce babu wani karancin shekaru ga wadanda ake yi wa fyade a jihar.

Ta kuma kara da cewa cikin wadanda aka yi wa fyade a baya-bayan nan har da wata jaririya 'yar wata tara da kuma wata tsohuwa.

Barista Hussaina ta ce a duk mako ana samun labarin fyade da aka yi wa mata da yara kusan sau 30 a Kano.

Image caption Jagoran zanga-zangar Husaina Ibrahim, ta ce ba babba ba yaro a wannan aikin assha na fyade da ake yi wa mata a Kano.

Al'amuran fyade dai na kara ta'azzara a jihar Kano da ma Najeriya baki daya, ta yadda ake barin matan da aka yi wa cikin wani hali na razana.