Tanzania ta haramta wa ma'aikata amfani da WhatsApp

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnati ta kare matsayinta kan wannan batun

Ma'aikatar sufuri da sadarwa ta Tanzania ta gargadi ma'aikatanta cewar za su iya rasa aikinsu, idan suna amfani da shafukan zumunta na zamani.

Minista a ma'aikatar Makame Mbarawa, ya ce gargadin zai taimaka wajen ingantuwar aiki da kuma kaucewa raba hankali a tsakanin ma'aikatan a lokacin aiki.

A cewarsa, ma'aikatar ya kamata ta zama abar koyi ga sauran ma'aikatun kasar.

Kamfanin wayoyin salula na samar da intanet ga jama'a a Tanzania a kan farashi mai rahusa, abin da ya sa shafuka kamarsu WhatsApp da Facebook da Twitter da Instagram suke da farin jini a tsakanin al'ummar kasar.