Kociyan Reading ya jinjina wa Alan Pardew

Image caption Kociyan Reading Brain McDermott abokin Perdew ne kociyan Crystal Palace, wadanda kulob din su za su fafata a ranar Juma'a

Kociyan kungiyar Reading, Brain McDermott, ya ce ba zai taba mantawa da mai horar da Crystal Palace ba, saboda dora shi a kan hanya da ya yi.

Sai dai su biyun za su kara a gasar cin kofin FA, a zagayen kusa da na daf da zagayen karshe a ranar Juma'a.

Sanayyar McDermott da Pardew ta soma ne a shekarar 1999, a lokacin da McDermott ya zama mai nemo 'yan wasa da kuma kula da 'yan kasa da shekara 17 a shekara 2000, ya kuma zama kociyan Reading a watan Janairu 2010.

McDermott ya yi shekara uku a karkashin Pardew kafin ya bar kulob din ya koma West Ham, a hirar da ya yi da BBC, McDermott ya ce "Ba don Alan ba, da ban kai matsayin da na ke a yanzu ba".