Zanga-zangar hura usur a Chadi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Idris Deby zai sake tsayawa takara bayan shafe shekaru 24 da ya yi yana mulki

Masu zanga-zanga a Chadi sun yi ta hura usur a gidajensu domin nuna cewa suna bukatar sahihin zabe a kasar a watan Afrilu.

Masu yakin neman zabe sun umarci mutane su hura usur din na tsawon mintuna 15 da misalin karfe 4.30 na asuba agogon GMT, su kuma sake yin hakan da yammaci.

Wadanda suka shirya hakan sun ce an yi tunanin yin zanga-zanga ne ta wannan salo ba tare da mutane sun fito kan tituna ba domin gudun abin da ka je ya zo.

Gamayyar kungiyoyin fararen hula 10 ne suka shirya wannan zanga-zanga ta lumana domin neman kawo karshen abin da suka kira gwamnatin zalinci da kuma neman sauyi a Chadi.

"Sanarwa a Facebook"

A wata sanarwa da mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin Celine Narmadji, ta sanya a shafinta na Facebook, ta ce, "Mutane su zauna a gidajensu ba tare da an ga masu hura usur din ba."

A watan Afrilu ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Chadi, inda shugaba Idris Deby wanda ya shafe shekaru 24 yana mulkin kasar zai sake takara tsayawa takara.

Karin bayani