Shekaru biyar da afkuwar Tsunami a Japan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekaru biyar da afkuwar annobar Tsunami

Al'ummomin kasar Japan na bukin tuna wa da mutanen da suka rasu a mummunar girgizar kasa hade da ruwa ta Tsunami data hallaka kimanin mutane dubu 20 shekaru biyar da suka gabata.

Wannan bala'i ya kuma janyo durkushewar tashar makamashi ta Fukushima,bayan da aka samu gurbacewar ruwa da abinci da kuma iska a yankin.

Ana saran Firaministan Shinzo Abe da Sarki Akihito za su ajiye furanni a dai-dai a wajen da ake gudanar da bikin zagoyar ranar a Tokyo.

Girgizar kasar mai karfin maurabbi'i tara ta haifar da mummunar ambaliyar a arewa maso gabashin kasar ta Japan.

Kazalika ta tursasawa mutane fiye da dubu 160 barin gidajensu, inda har yanzu mafi yawa daga cikinsu sun kasa dawowa gida

Gwamnatin kasar ta kashe biliyoyin daloli wajen aikin sake gina yankin da abin ya shafa, sai kuma har yanzu ba a kammala aikin ba, inda tuni daga cikin wadanda ke zaune a yankin da abin ya shafa suka fara rayuwarsu a wasu wuraren.

Ministan ayyuka na kasar Takagi Tsuyoshi ya yi alkawarin cewa za a kammala aikin sake gina wuraren inda ya ce zuwa nan da wasu shekaru biyar din za a kammala ginin