'Yan gudun hijirar tsibirin Lesbos

Wata 'yar jarida kuma mai hada fina-finai Daphne Tolis, ta bayar da labarin balaguron 'yan ci-rani da ke tsibirin Lesbos, ta shafinta ta na Instagram.

Kallon soyayya
Image caption 'Yan gudun hijirar Syria na jira ayi musu rajista a sansasnin Kara Tepe, da ke tsibirin Lesbos.

Lokacin da na zauna a tsibirin, ina ziyartar sansanonin Kara Tepe da Maria akalla sau daya a mako domin in ga halin da suke ciki, 'yan ci rani nawa ne ke jiran a yi masu rajista, da kuma wadanda ke hutawa kafin su dauki hanya.

Ba a yi wa sansanin Kara Tepe rajista ba, saboda haka hukumomin garin na amfani da shi a matsayin cibiyoyin tarba da kuma kula da lafiyar jama'a.

Lokacin da nake zagaye sansanin, domin ganin yadda ya kara fadi cikin 'yan makonni, sai naga wasu mata su biyu kowacce dauke da nata yaron, suna jira su shiga dakin ba haya.

Daya cikin matan ta mika wa 'yaruwarta nata yaron, saboda ta shiga dakin ba hayan.

Na tambaye ta ko ina iya daukar hoton su, sai ta nuna alamar amincewarta . Fuskanta akwai annashawa da fahimta, ta nuna matukar so da kauna.

Kukan zuci

A wannan ranar ba a samu shigowar jiragen ruwa da rana ba. A ranar ne kuma Ministan harkokin wajen Luxembourg da kwamishinan Majalisar tarayyar Turai kan harkokin 'yan ci rani, suka ziyarci tsibirin, domin rantsar da dandalin 'yan gudun hijirar, inda suka gana da jami'ai da wakilan Frontex.

Masu aikin kai agaji da masu bayar da gudunmuwa sun ce duk sanda jami'ai suka ziyarci tsibirin, sai ka ga jiragen ruwan sun rage shigowa da rana, sai dai kuma a fi samun shigowarsu da daddare.

An samu shigowar jirage ranar da yamma, tdauke da iyalai da kananan yara.

Ina zauna a gabar teku lokacin da wani jirga ruwa ya zo tare da wannan yaron. Yawancin lokuta kananan yara da jarirai na isowa cikin kuka a jiragen ruwan. Suna kuka tun daga cikin jiragen har zuwa lokacin da masu taimako za su sauke su. Cikin duhu da koke-koken yara, na yi kicibis da wannan fuska da ke da kwanciyar hankali, wanda kamar ya dakatar da hayaniyar koke-koken na dan mintuna.

Jirgin ruwan 'yan gudun hijira
Image caption Jirgi dauke da 'yan gudun hijira.

A watan Satumba, an samu karin jiragen ruwa biyu da ke shigowa da 'yan gudun hijira 4,000 daga tsibirin Lesbos zuwa tashar jiragen ruwa da ke garin Piraeus birnin Athens, a kullum.

Gwamnatin Girka ta dauki hayan wadannan jiragen ne na musamman saboda 'yan gudun hijira da 'yan ci rani, domin a rage cunkoso bayan mutane 20,000 da suka makale a Mytilene a farkon wata.

Da suke jira su shiga jirgin ruwa kashe gari, wadannan mazan sun tsaya a baya suna kallon jirgin ruwa cike makil da mutane ya nufi tsibirin Lesbos.

Tsallakawa zuwa Serbia
Image caption A wannan rana an samu daruruwan 'yan cirani da masu gudun hijira da suka ture jami'an tsaron Macedonia, suka baro Girka. Cikin hanzari suka shiga filin jiragen kasa da ke Gevgelija, duk da cewa sun sami jirgin a cike kuma. A hakan dai suka jajirce suka shige wani bas din da zai kai su wani wata kan iyakar da za ta iya kin karbar su.

Ranar 20 ga watan Agusta ne, Macedonia ta ayyana dokar ta baci kuma ta rufe kan iyakokinta da ke tsakanin ta da Girka.

Ranar 22 ga watan Agusta kuma daruruwan 'yan ci rani da masu gudun hijira suka yi nasarar tura dakarun sojojin Macedonia, suka samu fita daga Girka.

Dubban 'yan gudun hijira ne suka makale a tashar jirgin kasan Gevgelija, da ke Macedonia, suna jiran takardun da zai ba su damar shiga kasar a hanyar su ta tsallakawa zuwa Serbia.

Bayan an yi masu rajista, sai 'yan gudun hijirar su soma gasar neman kujeru cikin bas bas din da zata kai su kan iyakar Serbia.

"Ku koma Macedonia"
Image caption Wasu 'yan cirani da suka samu sauka daga jirgin kasa, a inda 'yan sanda Serbia ke tsawata masu, suna cewa "Ku koma Serbia".

Tawagar 'yan ci rani na tafiya kan layin hanyar da ke kan iyakar Macedonia da Serbia.

Wasu 'yan mitoci kafin layin tsallaka kan iyakar, ake jiyo 'yan sanda na tsawa da cewa "ku koma Macedonia"

Rajista
Image caption Wasu lambobi da aka rubuta a takarda, wanda zai basu damar shiga masauki su samu hutawa, da kuma abinci bayan sun tagayyara bayan kwana da kwanaki.

'Yan gudun hijira na jiran a kira lambarsu daga wajen wata cibiyar da ake rajista da kuma bayyana kai da ke Lesbos.

Akalla mutane 4,000 ne ke isowa ta hanyoyin ruwa a watan Satumba, inda a wasu lokutan har sai su yi kwana da kwanaki suna jiran takardar rajistar da za ta basu damar baro tsibirin su kama hanyar Athens.

Hawa jirgin kasa
Image caption 'Yan gudun hijira da ke jirgin kasa a Gevgeljia. Idan har suka samu shiga, to zasu sauka ne a kan iyakar Serbia, su kuma nausa kasar Hungary, wacce ta sa shingaye a kan iyakarta.

Kwanaki kadan bayan hayaniyar tashar jirgin Gevgelija, inda daruruwan 'yan gudun hijira ke makare cikin jiragen kasa, har da wasu ma cikin a kori kurar jirgin, jami'an sufurin Macedonia sai su tatance takardun nasu.