Myanmar na shirin bayyana shugaban kasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Aung San Suu Kyi, tare da Htin Kyaw, wanda shi ne dan hannun daman ta.

A Myanmar, jam'iyyar National League for Democracy wadda ta mamaye kujerun majalisar dokokin kasar ta mika sunayen mutum biyu da take so a nada musu mukamin mataikama shugaban kasa.

Daya daga cikin su shi ne Htin Kyaw, wani na-hannun-daman shugabar jam'iyyar, Aung San Suu Kyi.

Babu damar mika sunan Aung San Suu Kyi, kasancewar kundin tsarin mulkin kasar, wanda sojoji suka rubuta, ya haramta mata rike mukami a fadar shugaban kasa.

Sojojin kasar ne za su mika sunan mutum na uku.

Wakilin BBC ya ce da yiwuwar Htin Kyaw zai samu shiga fadar shugaban kasar, inda zai kasance dan amshin-shatan Mis Aung San Suu Kyi.