Farfesa Jega ya gana da 'yan adawar Nijar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jega ya tattauna da 'yan adawar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa zagaye na biyu, offishin jakadancin Amurka ya shirya wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar zabe a wani mataki na kaucewa duk wasu matsaloli a lokacin zaben.

Daga cikin wadanda suka gana da 'yan siyasar kasar da kuma shugabannin hukumar zaben Nijar din wato CENI, har da tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega.

Farfesa Jega ya samu tattaunawa da bangarorin siyasar ta Nijar.

Ga dai abinda ya shaidawa manema labarai dangane da tattaunawar ta su da bangarorin 'yan adawar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti