An yi gwajin maganin sankarar mama a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Sankarar mama ta halaka mata da dama

Likitoci a Biritaniya sun ce sun yi gwajin wasu kwayoyin magani biyu, da za su iya rage, ko kawar da cutar sankarar mama a cikin kwanaki 11 kacal.

Duk kan kwayoyin maganin biyu, Lapatinib da Herceptin, suna kashe sinadarin protein da ake kira HER2.

An yi gwajin amfani da magungunan biyu tare a London da Manchester, a kan fiye da mata 250 da suke dauke da cutar ta sankarar mama.

Bayan kwanaki 11, an gano cutar ta ragu sosai a jikin akasarin matan.

Likitocin sun ce idan har wannan bincike na su ya yi nasara a karin gwaje-gwaje da za a yi, mata da yawa za su samu sa'ida.