Sojojin Amurka sun cafke yaron Saddam

Sojin Amurka a bakin aiki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Suleiman Daoud na hannun daman marigayi Saddam Hussein ne.

Rahotanni na cewa sojojin Amurka sun cafke Suleiman Daoud al-Afari, wani kwararren da ke hada makami mai guba, wanda ya yi wa Saddam Hussein aiki, amma yanzu ya shiga kungiyar IS.

An dai kama Suleiman Daoud al-Afari ne a wani samame da sojojin Amurkan suka kai a watan jiya.

Yanzu dai ana rike da shi a wani wuri a arewacin kasar Iraki, inda ake masa tambayoyi a kan yunkurin da mayakan Is din ke yi na hada makami mai guba .

A watan jiya ma, wasu kwararru sun ce mayakan IS din sun yi amfani da wata guba lokacin da suka kai hari kan mayakan Kurdawa a arewacin Irakin.

Har yanzu dai ma'aikatar tsaron Amurka ba ce komai a kan cafke Suleiman Daoud al-Afarin ba.