Wata ta boye yarinya a jakar matafiya

Image caption Matar ta hau jirgi ne daga Turkiyya zuwa Faransa

An kama wata mata da ta boye yarinya dan shekara hudu a jakar matafiya, yayin da take tafiya daga Turkiya zuwa Faransa.

An gano yarinyar ne lokacin da fasinjoji suka lura cewa jakar da ke kusa da kafar mata a ajiye na motsawa.

Ana zargin cewa matar, wadda mazauniyar Faransa ce ta dauko yarinyar ne daga Haiti domin ta rike ta, amma ba ta da cikakkun takardun bayar da izini.

Yanzu haka dai ana bai wa yarinyar kulawa, matar kuma na tsare a filin jirgin saman Pais amma ba a tuhumeta da laifin komai ba tukunna.