Bayan shekara 40: Shugaban Angola zai sauka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A shekara mai zuwa ne za a gudanar babban zabe a kasar

Shugaban kasar Angola, Jose Eduardo dos Santos, ya ce yana shirin sauka daga mulki a shekarar 2018, bayan ya shafe kusan shekaru 40 yana shugabancin kasar.

Shugaban ya sanar da hakan ne a wani jawabi da ya yi a gaban babban kwamitin jam'iyyar MPLA mai mulkin kasar.

A shekara mai zuwa ne za a gudanar babban zabe a kasar.

A shekara ta 2001, Mista Dos Santos ya sanar da cewa ba zai sake tsaya wa takara a zaben shugaban kasar na gaba ba, sai dai kuma ya ci gaba da zama a kan karagar mulki.

Angola ce kasa ta biyu a Afirka, cikin mafiya safarar mai zuwa kasuwannin duniya, kuma ta fuskanci matsalar tattalin arziki saboda faduwar farashin man.

Yanzu haka, kasar tana tattaunawa da bankin duniya da kuma hukumar bayar da Lamuni ta duniya kan yadda za su tallafa mata.

Karin bayani