Sojoji sun tarwatsa sansanin Boko Haram da ke Alajeri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Najeriya na samun nasara a kan mayakan boko haram

Dakarun sojin da ke yaki da 'yan kungiyar boko haram a Najeriya, sun samu nasarar shiga yankin Dunga a ranar Alhamis, inda suka samu nasarar tarwatsa wani sansanin 'yan kungiyar ta boko haram da ke kauyen Alajeri da ke karamar hukumar Guzamala a jihar Borno.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka Sheka , ta ce a lokacin da suka kai samamen, dakarun sun kashe 'yan boko haram arba'in, tare da samun makamai da suka hada da bindigogi da alburusai da wayoyin salula uku da Babura da kuma littattafan Al-Qur'ani guda shida.

Dakarun sojin dai na cike da kwarin gwiwa saboda irin nasarar da suke samu a yaki da 'yan kungiyar ta boko haram, sannan kuma a wannan karon ba a kashe ko jikkata daya daga cikin sojojin ba.

Kazalika sanarwar ta ce wasu dakarun nata sun gwabza da mayakan na boko haram a kauyen Ma'ala da ke karamar hukumar Kukawa a jihar ta Borno, inda suka kashe dan boko haram guda tare da kama guda a raye.

Sannan sun ceto wata yarinya 'yar kimanin shekaru uku daga wajen masu tada kayar bayan.