Saraki ya je kotu da Lauyoyi 66

Shugaban majalisar dattawan Nigeria, Sanata Bukola Saraki ya bayyana a gaban kotun kula da da'ar ma'aikata da ke Abuja tare da sanatoci da manyan lauyoyi masu yawa.

Ana tuhumar Sanata Saraki da aikata laifuka 13 da suka hada da kin bayyana kadarorinsa, zargin da ya musanta

Wannan ne karo na hudu da shugaban majalisar dattawa ke bayyana gaban kotun kula da da'ar ma'aikata.

Ibrahim Mijinyawa ya tambayi Haruna Shehu Tangaza, wanda ya halarci zaman kotun na yau, abin da ya faru a kotun, kuma ko shi Shugaban Majalisar dattawan ya bayyana da kansa?

Ga karin bayanin da ya yi masa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A watan Fabrairu ne Sanata Saraki ya kai kotun kula da'ar ma'aikatan gaban kotun kolin, inda yake so ta hana ta tuhumarsa, yana mai cewa ba ta da hurumin sauraren kara a kansa.

Sai dai kotun kolin ta ce kotun kula da da'ar ma'aikatan tana da hurumin yi masa shari'a.