"Soji sun kashe mutane da gangan a Sudan ta Kudu"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sha zargin sojojin Sudan ta Kudu da aikata laifukan yaki

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta zargi sojoji a Sudan ta Kudu da kisan wasu mutane fiye da 60 da gangan.

Sojojin dai sun saka mutanen cikin wani sunduki da suka rufe ruf har sai da numfashinsu ya dauke a wani yanayi na tsananin zafi.

Amnesty ta ce lamarin ya afku ne a harabar cocin Katolika da ke garin Leer, a watan Oktoban bara.

Gwamnatin Sudan ta Kudu dai ta musanta mutuwar mutanen, sai dai kungiyar ta ce ta samu wasu shaidu fiye da 20 da suka bayyana cewa, sun ji lokacin da mutanen ke ta kururuwa saboda rashin iska a inda aka rufe su.

Shaidun sun kuma bayyana cewa mutanen da aka hallaka 'yan kasuwa ne da dalibai amma ba mayaka ba.

Karin bayani