Trump ya soke taron gangami a Chicago

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An soke gangamin Trump

An soke wani gangamin yakin neman zabe a Chicago na dan takarar shugabancin Amurka da ke sahun gaba a karkashin inuwar jam'iyyar Republican, Donald Trump, saboda zanga-zangar da aka yi.

Akwai kuma wasu dubban jama'a da suka yi zanga-zanga a waje inda wasun su ke zargin dan takaran da nuna wariyar launin fata.

Sai dai Kwamitin yakin neman zaben Mr Trump ya ce ya soke gangamin saboda rashin tsaro inda ya bukaci jama'a da su zauna lafiya, yayin da a nasa bangaren Mr Trump ya musanta cewa kalaman da yake yi na assasa tashe- tashen hankula.

A cikin wajen kuwa fada ne ya barke tsakanin magoya bayan Mr Trump da kuma masu zanga-zanga wadanda ke daga tuta suna ife-ifensu.

Daga cikin masu zanga-zangar akwai magoya bayan dan takarar shugabancin kasar ta Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat wato Bernie Sanders, wadanda suma ke daga hotunan dantakararsu ta re da wake-wake