Za'a gudanar da zaben yankuna a Jamus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a gudanar da zaben yankuna a kasar Jamus

Al'ummomin kasar Jamus zasu kada kuri'a a zaben yankuna da ake gani zai kasance zakaran gwajin dafi na goyon bayan manufofin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan 'yan gudun hijira.

Fiye da mutane miliyan daya ne suka nemi mafaka a kasar ta Jamus a shekarar da ta gabata.

Sai dai a 'yan watannin nan an yi ta nuna rashin gamsuwa game da shawarar Mrs Merkel ta yin marhabin ga mutanen da suka tsere wa yakin basasa a kasar Syria.

Da aka tambayi Mrs Merkel game da yadda ta shirya wa zaben sai tace ta zuba idanu ta ga yadda zaben zai kasance.

Za'a gudanar da zabubbukan ne a jihohi uku da suka hada da Rine land Palatinate, da Baden Vuttemberg, da kuma ZACK-Suhn AN-halt.