An kai hari a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara

An kai hari a wani otel mai suna Grand Bassam da ke bakin gabar teku, kusa da Abidjan babban birnin Ivory Coast.

Rahotanni na cewa an jikkata mutane da yawa a otel din mai farin-jini wurin masu yawon bude-ido.

Babu cikakken bayani kan harin a yanzu, kuma ba a san wadanda suka kai harin ba, sai dai wasu da al'amarin ya faru a kan idonsu na cewa sun ji maharan na yin kabbara yayin da suke kai harin.

Mahunkuta kasar sun bayyana harin a matsayin harin ta'addanci