Nigeria: CBN ya dakatar da daraktoci uku

Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya matsa kaimi wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar

Gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu manyan jami'an babban bankin Najeriya CBN bisa zargin almundahana na daruruwan miliyoyin daloli.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari shi ne ya bada umarnin dakatar da ma'aikatan na CBN wadanda suka hada da wani mataimakin gwamnan bankin da wasu daraktoci uku.

Wata majiya daga fadar shugaban kasar ta ce mataimakin gwamnan bankin, tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan shi ne ya nada shi kuma yana daga cikin mutanen da aka ambato a ci gaba da binciken sama da fadi na wasu kudade da suka kai dala miliyan 400.

Wata sanarwa da babban bankin CBN ya fitar a daren jiya ya tabbatar da cewa an bankado shirin wasu mazambata na damfarar bankin na CBN an kuma dakile wannan yunkuri.

Sanarwar wadda mukaddashin daraktan sadarwa Isaac Okorafor ya sanyawa hannu ta ce babban bankin ya dakatar da ma'aikatan wadanda ba a bayyana sunayensu ba domin samun damar gudanar da cikakken bincike game da rawar da suka taka a almundahanar.