NDLEA ta kama masu sarrafa miyagun kwayoyi

Hakkin mallakar hoto NDLEA
Image caption NDLEA ta ce akwai 'yan Nigeria guda hudu da kuma wa su 'yan kasar Mexico su hudu da aka kama

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, wato NDLEA ta kama wasu mutane da ke sarrafa hodar Iblis da ake kira Methampitamin mafi girma a Najeriya.

Hukumar ta ce ta samu nasarar kame mutanen ne a wani kamfanin da suke sarrafa hodar bayan wata mamaya da ta kai kamfanin da ke garin Asaba, babban birnin jihar Delta.

A wata hira da BBC, shugaban hukumar ta NDLEA Colonel Muhammadu Mustapha Abdallah mai ritaya, ya ce akwai 'yan Nigeria guda hudu da kuma wa su 'yan kasar Mexico su hudu da aka kama a kamfanin da suke sarrafa kwayoyin da ke da illa ga jama'a.

A baya dai Hukumar ta NDLEA ta nemi da a tsaurara hukunci a kan masu ta'ammali da miyagun kwayoyi a kasar.