Turkiyya:An lakada wa yan gudun hijira duka

Hakkin mallakar hoto

Wani wakilin BBC a Girka ya ga wani faifan bidiyo inda wasu mutane a cikin wani jirgin ruwa suke dukan wasu mutanen da ke cikin jirgin kwale kwale da kulake yayinda jirgin ke ketara wa da yan gudun hijira a kogin Aegean daga Turkiyya.

Faifan bidiyon ya fito ne daga wani ma'aikacin sa kai da ke tsibirin Lesbos a Girka.

Wani jami'in tsaron gabar ruwa na kasar Turkiyya ya tabbatarwa da BBC cewa wani jirgin tsaron ruwan Turkiyya na cikin lamarin.

Sai dai yace ma'aikatan jirgin na kokarin tsayar da injin kwale kwalen yan gudun hijrar ne ba tare da ya cutar da fasinjojinsa ba saboda a jawo jirgin domin maida shi zuwa Turkiyya.

A farkon wannan makon ne dai Turkiyya da shugabannin kungiyar tarayyar turai suka cimma yarjejeniya a kan wasu sabbin matakai masu tsauri domin dakile kwararar yan gudun hijira.