Buhari ya isa birnin Malabo

Hakkin mallakar hoto Nigeria
Image caption An yi wa Buhari faretin ban girma a Malabo

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya isa birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea domin soma wata ziyara ta kwanaki biyu inda zai tattauna da takwaran aikin sa Shugaba Obiang Nguema Mbasogo game da samar da tsaro a yankin mashigin tekun Guinea.

Ana sa ran shugabannin biyu za su kammala tattaunawa a kan wata yarjejeniya ta samar da rundunar tsaron yankin ta hadin gwiwa.

Yankin na mashigin tekun Guinea dai na fama da hare-haren 'yan fashi a teku, lamarin da ke ciwa kasashen yammacin Afirka da ma na duniya tuwo a kwarya.

Mataimaki na musamman ga Shugaba Buhari a kan al'amuran yada labarai, Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa ziyarar tana da matukar muhimmanci ga Najeriyar.