A daina boye lafiyar matuka jirgin sama

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban kwamitin binciken hadarin jirgin saman Germanwings da ya faru a bara, ya yi kira ga likitoci su baiyana halin da lafiyar majinyatansu ke ciki musmaman idan zai jefa rayuwar al'umma cikin hadari.

Arnaud Desjardin na cibiyar bincike ta Faransa yace barin matuka jirgin sama su baiyana tsarinsu na tantancewar lafiyar ya gaza.

Maitaimakawa matukin jirgin sama Andreas Lubitz da gangan ya tuka jirgin da ya fadi a tsaunukan Faransa da ya hallaka dukkan mutane 150 da ke cikinsa.

Wani likita wanda ya duba shi 'yan makonni kafin hadarin ya tura shi ga likitan kwakwalwa amma bai sanar da wadanda suka dauke shi aiki ba.