Masu kayan gwari sun koka da rufe kasuwar mile 12

Image caption Masu kayan miya na tafka asara saboda rufe kasuwar Mile 12

Masu sana'ar safarar kayan miya daga arewacin Nigeria zuwa jihar Lagos a kudanci sun ce su na tafka asarar daruruwan miliyoyin Nairori a kullum sakamakon rufe kasuwar mile 12 da hukumomin jihar Lagos suka yi tun bayan wani rikici da aka yi a kasuwar a kwanakin baya.

Yan kasuwar sun ce matakin ya shafi daruruwan yan kasuwa, da manoma da kuma diroboin motoci.

A yanzu haka dai wannan kulle kasuwar na daya daga abubuwan da suka janyo mummunar asarar kayan miya musamman ma dai tumatur ga manoman rani dake jihar Kano a arewacin Nigeria.

Saboda asarar da ake tafkawa dai a kullum ta sama da Naira miliyan dari hudu a cewar shugabannin masu harkar kayan miyan, dole suka dauki matakin neman hukumomi su sa baki ko gwamnatin jihar Lagos zata gaggauta bude kasuwar ta mile 12.

To sai dai a bangaren majalisar dokokin jihar Kano a ta bakin mataimakin shugaban ta Eng. Hamisu Ibrahim za su duba hanyoyin da ya kamata domin kawo karshen matsalar.

Bayanai dai na cewa ba a taba yin noman tumatur a yankin da ake noman rani na kudancin Kano ba kamar wannan shekarar, musamman ma da manoman suke sa ran kamfanin sarrafa tumatur na Dangote zai fara aiki, wanda suke sa ran zai saye tumatur din na su.

Sai dai kuma rashin fara aikin kamfanin, da kuma rufe kasuwar mile 12 sun sa manoma da dama ke gwammacewa su bar tumatur din a gona ya lalace, dan kar su kara yi masa wata wahala da za ta kara musu asara.

To amma manoman suna da kyakkaywar fata cewa matukar kamfanin na Dangote ya fara karbar tumatur din su a kowanne lokaci daga yanzu, to za su iya rage asarar da suke tafkawa.