Sojoji sun tarwatsa sansanonin BH

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Sojojin Najeriya sun yi nasarar tarwatsa sansanonin mayakan Boko Haram a wasu sassa na jihar Borno

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce dakarunta da hadin gwiwar 'yan kato da gora sun kawar da birbishin 'yan Boko Haram daga kauyen Gwashari, a kan hanyar Damboa zuwa Bale a jihar Borno.

A wata sanarwa da ta fito daga kakakinta, Kanar Sani Usman Kuka Sheka, rundunar ta ce yayin kaddamar da harin -- dakarun sun yi arangama da wa su mayakan Boko Haram din, wadanda aka kashe daya daga cikinsu aka kuma kama uku.

Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun kuma kwato bindiga harbi-ka-ruga guda daya, da albarusan bindiga AK-47 da wukake guda biyu da wasu magunguna da kuma kudi Naira 140,000.

A 'yan kwanakin nan dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar tarwatsa sansanonin mayakan Boko Haram a wasu sassa na jihar Borno, tare da hallaka wasu mayakan kungiyar da dama.