Mutane 34 sun mutu a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kai hari a Ankara na kasara Turkiyya

Ministan lafiya na kasar Turkiyya Mehmet Muezzinoglu ya ce akalla mutane talatin da hudu sun rasa rayukansu bayan da wani bam mai karfi ya fashe a tsakiyar Ankara babban birnin Turkiyya.

Sannan wasu akalla dari da ashirin da biyar sun samu raunuka.

An dai ji karar fashewar bam din a sassan birnin inda daga bisani kuma aka rinka hango hayaki na tashi daga wajen da abin ya faru.

Rahotanni sun ce bisa ga dukkan alamu hari ne na kunar bakin wake da aka dasa bam din a cikin wata karamar mota.

Harin ya kona motoci da dama a kusa da wata tashar Bus a gundumar Kizilay.

Kazalika an kuma sami rahoton harbe-harben bindiga bayan fashewar bam din.

Ministan cikin gidan kasar Efkan Ala ya ce nan bada jimawa ba bayan an kammala bincike za a bayyana sunan kungiyar da ta kai harin.

A watan da ya gabata ma an kai harin bam birnin na Ankara wanda ya hallaka mutane kimanin talatin.

Wata kungiyar 'yan tawayen Kurdawa ta ce ita ce ta kai harin.