Adamawa: Za a yi bincike kan rikicin maharba

Gwamnatin jihar Adamawa a arewacin Nigeria, ta ce ta kafa wani kwamitin bincike don gano musababbin abin da ya janyo rikici tsakanin wasu kungiyoyin maharba guda biyu, da basa ga-maciji-da juna a garin Gombi.

Sai dai ta ce har yanzu, ba ta kai ga tantance yawan mutane da suka rasa rayukansu a cikin tashin hankalin ba.

Ga rahoton da Raliya Zubairu ta hada mana kan batun:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A ranar Asabar din da ta gabata ne kungiyoyin maharban suka yi fada a wajen wata nadin sarauta, inda rahotanni suka ce an rasa rayuka kuma mutane da dama sun jikkata.