Amnesty: Bore a ofisoshin jakadancin Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Amnesty International ita ce kungiyar da ke kokarin kare hakkin bil'adama a duniya.

Kungiyar kare hakkin Bil'adama ta amnesty International za ta yi zanga-zanga a wajen ofisoshin jakadanci Najeriya da ke kasashen duniya baki daya.

Kungiyar ta dauki wannan mataki ne shekaru biyu bayan ta yi zargin cewar, sojojin Najeriya sun yi wa mutane 640, wadanda suka kwato daga inda ake tsare da su yankan rago.

An kashe mata da maza ne wadanda ake tsare da su a lokacin da suka tsere daga barikin sojoji da ke birnin Maiduguri, a Jihar Borno, a ranar 14 ga watan Maris shekarar 2014, bayan wani harin 'yan Boko Haram.

Shugaban sashen bincike na kungiyar Amnesty International, Netsanet Belay, ya ce, "Abin firgitarwa shi ne, shekara biyu bayan wadannan munanan kashe-kashe, ba a yi wa wadanda abin ya shafa da kuma 'yan uwansu adalci ba."

Mista Netsanet ya kara da cewa, "Rashin bincike mai zaman kansa, na nufin cewa babu wanda aka kama da laifin kashe-kashen da aka yi, wanda haka zai karfafa wa sojojin su ci gaba da cin karensu ba babbaka.

Kungiyar ta yi zargin cewar gwamnatin shugaba Buhari ta yi alkawarin duba rahoton da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International din ta fitar, sai dai babu wasu kwararan matakai da ta dauka domin fara binciken.